25 Yuli 2024 - 08:36
Adadin Shahidai A Zirin Gaza Ya Kai Mutane Dubu 39145

Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da alkaluman kididdiga na baya-bayan nan na shahidai da wadanda suka jikkata sakamakon laifukan yakin ta’addanci da gwamnatin sahyoniyawan ke yi a zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya habarta maku bisa nakaltowa daga Kamfanin dillancin labaran Irna cewa: ma'aikatar lafiya ta kasar Falasdinu ta sanar da cewa: A cikin sa'o'i 24 da suka gabata gwamnatin sahyoniyawan ta yi kisan kiyashi a zirin Gaza har sau 3, wanda a sakamakon hakan mutane 55 ne suka yi shahada tare da wasu 110 na daban da su ka jikkata.

Bisa ga wannan rahoto da suka hada da wadannan shahidai, adadin shahidan a Gaza ya kai mutane dubu 39145, yayin da adadin wadanda suka jikkata ya kai dubu 90257 tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023, a daidai lokacin da aka fara Dufanul Al-Aqsa.